Kiwon Lafiya
Sambo Dasuki:ya gurfanar da darakter hukumar DSS da Attorney janar na kasa
Tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro kanal Sambo Dasuki mai ritaya, ya gurfanar da daraktan hukumar tsaron sirri ta DSS Lawal Daura da Attorney Janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami gaban kotu, yana mai zargin su da danne masa hakki na kasancewar sa bil’adama.
Cikin takardar karar da lauyan Dasuki ya gabatar gaban babban kotun tarayya da ke Abuja, ya zargi hukumar ta DSS da ta ke masa hakkin sa na bil’adama sakamakon ci gaba da tsare shi da take.
Haka zalika Sambo Dasuki ya kuma bukaci kotun da ta tursasa mutanen biyu da su biya shi diyyar naira biliyan biyar.
Hukumar tsaro ta DSS dai tana tsare da Sambo Dasuki ne tun a ranar 29 ga watan Disamban shekarar dubu biyu da sha biyar.
Sai dai wata kotun yammacin Afurka yayin wani hukuncin da ta bayar a ranar hudu ga Oktoban shekarar 2016 ta ce ci gaba da tsare Sambo Dasuki haramun ne.