Nishadi
Sanadin TikTok na soma sayar da maganin mata – Mai Wushirya
Tauraron TikTok Ashir Idris da aka fi sani da Mai Wushirya ya ce, sakamakon TikTok ya shiga sayar da magungunan mata.
A zantawarsa da tashar Dala FM da ke Kano, Idris ya ce, ya soma ne da yiwa wasu talla kafin daga bisani ya rikiɗe.
Idris ya ce, ya ce ya samu riba mai yawa a sanadin TikTok.
Ya ce, baya damuwa da waɗanda ke zaginsa, ko kiransa da ɗan daudu, domin hakan alamun nasara ne a wajensa.
Da yake martani kan haɗewar Murja Ibrahim Kunya da mawaƙi Mr442 mai Wushirya ya ce, tafiyarsu da ita ba zata yi ƙarko ba.
Yayin tattaunawar dai Ashir Idris ya bada tarihin rayuwarsa da kuma dalilin shigarsa TikTok.
Kuna iya kallon cikakkiyar tattaunawar yanzu haka a shafin YOUTUBE na tashar Dala FM Kano.
You must be logged in to post a comment Login