Labarai
Sanata Dino Melaye ya halarci zaman majalisar dattijai a yau laraba
Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye ya isa zauran majalisar dattijai a yau laraba bayan makonni da dama da ya dauka bai hallacci zaman majalisar ba.
Mr. Melaye dai na kwance ne a asibiti tun lokacin da ya yi yunkurin guduwa daga hannun jami’an yan sanda lokacin da suke kokarin tafiya da shi jihar Kogi.
Da ya ke jawabi a zaman majalisar na yau, Melaye ya godewa abokan aikin sa, da yan majalisar wakilai da jama’ar yankin sa, da ya ke wakilta da sauran al’ummar kasar nan da suka jajirce wajen tabbatar da cewa bai fada gadarzaren da aka shirya masa ba.
Haka kuma ya godewa shugabancin jam’iyyar PDP kan irin goyon bayan da suka bashi.
Mr Melaye ya isa majalisar a yau ne da abinda ke tallafa masa wajen tsayar da wuyansa, inda kuma yayi kira ga shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da ya sama masa kujera a bangaren mambobin majalisar da ke karkashin Inuwar jam’iyyar PDP.
Daga nan kuma sai ya ce zai zauna kusa da tsohon shugaban majalisar Sanata David Mark kafin lokacin da za’a sama masa Kujerar da zai rika zama a tsagin mambobin Majalisar da ke karkashin Inuwar jam’iyyar PDP.
Hakan dai ya jawo cece-ku-ce a majalisar sakamakon zargin da wasu mambobin majalisar ke yi na cewa zai Sauya Sheka zuwa jam’iyyar PDP sai dai shi Sanata Dino Melaye bai bayyana cewa ya koma jam’iyyar ta PDP ko akasin hakan ba.