Connect with us

Labarai

Sanata Kawu Sumaila ya fice daga jam’iyyar NNPP

Published

on

Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP ba tare da komawa wata jam’iyyar ba.

Wata sanarwa da mai taimaka wa Sanatan na musamman kan harkokin yada labarai Abbas Adam Abbas ya fitar a daren yau Laraba, ta ruwaito cewa Kawu Sumaila ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma makusantansa.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa Kawo zai bayyana jam’iyyar da zai koma a nan gaba.

Sanarwar ta ce, Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, ya jaddada aniyarsa ta sadaukar da Kai wajen yin ayyukan da za su amfani al’umma tare da, alkawarin ci gaba da kare muradun al’ummar Kano ta Kudu, da fifiko ga bukatu da burinsu a tafiyar da yake yi ta siyasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!