Labarai
Sanatoci sun zargi hukumomin gwamnati da kin sanya naira tiriliyan 2 a asusun tarayya
Majalisar dattijai ta zargi wasu hukumomi da sassan gwmanatin tarayya da kin sanya kudade a asusun gwamnati da ya kai jimillar sama da naira tiriliyan biyu.
Kwamitin kula da harkokin kudi na majalisar shine yayi wannan zargin yana mai cewa wannan al’amari ya faru ne tsakanin shekarar 2014 zuwa yanzu.
Shugaban kwamitin kula da harkokin kudi na majalisar dattijai sanata Solomon Adeola shine ya bayyana hakan lokacin da ‘yan kwamitin ke ganawa da ministar kudi kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed da akanta janar na kasa Ahmed Idris da kuma daraktan kula da ofishin kasafin kudi na tarayya Ben Akabueze.
A cikin wani faifan bidiyo na tattaunawar da ‘yan kwamitin majailsar dattijan suka sake a jiya lahadi, ya nuno shugaban kwamitin kula da harkokin kudi na majalisar dattawan sanata Adeola na cewa, rashin sanya kudaden a asusun tarayya ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da kuma dokokin kudi na shekarar 2007
You must be logged in to post a comment Login