Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sanusi Ƙiru ya ajiye Kwamishina, ya shiga tseren takarar majalisar tarayya

Published

on

Kwamishinan ilimi na Kano Alhaji Sanusi Sa’idu Ƙiru ya sauka daga muƙaminsa don takarar ɗan majalisar tarayya a Ƙiru da Bebeji.

Mai taimakawa Gwamnan kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamna Ganduje ya bai wa masu riƙe da muƙaman siyasa da ke sha’awar takara umarnin ajiye aiki domin biyayya ga dokar zaɓe.

Kawo yanzu Kwamishinoni shida ne suka ajiye muƙamansu a yau, tare da wasu daga hadiman Gwamnati da zimmar tsayawa takara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!