Labaran Kano
Sanyin Kano da na Ingila basa kamanceceniya – Masani
Bayanan dake zagawa a satin da ya gabata a kafofin sadarwa na cewa sanyin Kano ya fi na Ingila ko kuma hasashen za’a yi kankara a Kano ba gaskiya bane.
Masanin muhalli daga Jamiar Bayero ta Kano Dr Aliyu Salisu Barau ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hansti na nan tashar Freedom Radio.
Dr Aliyu Salisu Barau yace wasu daga cikin al’umma suna yin kuskure wajen fassara yadda yanayi ke kasancewa .
Yace ma’aunin Celsius a mataki na 9 da ake cewa Kano ta kai matsayi ne na ma’aunin sanyi da Kano kadai zata iya kaiwa.
Yace irin sanyin da ke faruwa a wannan sati a Kano lokacin sanyi ne da ke tahowa daga arewa kuma iskace busashshiya saboda haka tana dauke da sanyi mai tsanani ba kamar iska mai tahowa daga Kudu ba.
Bayan haka yace a sati biyu da suka wuce akwai bayanai da suke bayyana cewa za’a samu irin wannan sanyi a nan Kano da wasu sassan arewacin Najeriya.
Dr Aliyu Salisu Barau yayi kira ga al’umma da su kiyaye akan muamala da kayan wuta da sauran abubuwa.