Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Sa’o’i kadan ya rage Najeriya ta karbi rigakafin Corona – Boss Mustapha

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa a gobe Talata ne za ta karɓi kason farko na alluran rigakafin korona ta Oxford-AstraZeneca kimanin miliyan hudu.

Sakataren Gwamnatin tarayya kuma shugaban, kwamitin yaki da cutar corona na shugaban kasa Boss Mustapha ne ya bayyana hakan cikin wani sakon bidiyo da ya aikewa manema labarai.

Ya ce Najeriya za ta karɓi rigakafin ne ƙarƙashin shirin hukumar lafiya ta duniya WHO da ake kira COVAX na rarraba rigakafin ga ƙasashen duniya.

Gwamnatin wadda a baya ta sanar da cewa alluran rigakafin za su iso kasar nan a karshen watan Fabrairu, daga bisani ta ce mai yiwuwa a cikin makon farko na watan Maris.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!