Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarki Aminu Ado Bayero ya buƙaci dakarun Najeriya su kara kaimi don inganta tsaro

Published

on

Mai martaba Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci jami’an tsaron Nijeriya su mai da hankali wajen samar da tsaro mai inganci a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Sarkin ya bukaci hakan ne ayayin da ya karbi bakuncin sabon Kwamandan rundunar sojojin sama ta 455 da ke Kano, Group Captain Mustapha Suleiman a fadarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci masu taimakawa sabon shugaban sojojin sama dasu bashi cikakken hadinkai don samun nasarar gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali.

A nasa jawabin sabon kwamandan hukumar rudunar sojojin sama ta kasa shiyar jihar kano Group Captain Mustapha Suleiman ya ce sun zo fadar mai martaba Sarkin ne domin gaisuwar ban-girma da gabatar da kansa tare da neman albarkar masarautar Kano da Sarkin.

 

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!