Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarki Aminu Ado Bayero ya jajantawa yan kasuwar Singa

Published

on

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, JP, ya jajanta wa yan kasuwar Singa da ke cikin birnin Kano bisa iftila’in gobara da ta tashi a kasuwar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa.

Sanarwar ta ruwaito cewa, Mai Martaba Sarki ya nuna damuwarsa matuka a lokacin da ya samu labarin tashin gobarar.

Haka kuma Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake mika sakon jajantawa ga yan Kasuwar Kurmi da Kasuwar Rimi su ma bisa ifila’in gobara da suka samu a kwanakin baya.

Sarkin ya taya su jajantawa da nuna alhini tare da yin addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.

Wakilinmu na masarautar kano Shamsu Da’u Abdullahi ya ruwaito cewa mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga yan kasuwar da kungiyoyinsu kan su ci gaba da yawaita adduo’o’i da kuma daukar dukkan matakan kare afkuwar irin wannan iftila’I a ko da yaushe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!