Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasu daga cikin muhimman al’amuran da suka faru a masarautar Kano a 2022

Published

on

  • A shekarar ne masarautar ta gudanar da hawan Daba domin taya sarki murnar samun lambar girmamawa ta CFR.
  • Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
  • Sarki ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa a APC Bola Ahmed Tinubu.

A shekarar da muka yi ban kwana da ita ne masarautar Kano ta gudanar da wani gagarumin hawan daba na musamman, domin taya sarkin murna a kan lambar karramawa ta kasa ta CFR da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi, da kuma wadanda aka ba shi a kasashen Senegal da Morocco.

Tarin jama’a ne daga nan gida Najeriya da kuma kasashen waje, ciki har da mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna suka halarci taron bikin.

A cikin shekarar ne mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya zo Kano don jajantawa al’ummar jihar, game da ibtila’in da ya faru na fashewar tukunyar gas a yankin Sabon Gari na karamar hukumar Fagge, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane.

Sarkin wanda ya bayyana gamsuwarsa da da jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, musamman wajen inganta rayukan al’umma, ya ce wannan ziyara da shugaban kasa ya kawo Kano ta nuna irin yadda ya damu al’ummar jihar.

Da yake na sa jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa mai martaba sarki cewa ya zo Kano ne domin yi wa sarki ta’aziyya sakamakon rasuwar mutanen da aka samu sanadiyyar fashewar tukunyar gas a Sabon Gari, tare kuma da halartar taron bikin cika shekaru 58 da rundunar sojojin Najeriya ta yi.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma manyan jami’an gwamnatin tarayya.

A shekarar da muke ban kwana da ita ne sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a fadarsa.

Haka zalika a cikin shekarar ne mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya sabunta lasisin tukinsa don kiyayewa da dokokin ababen hawa.

Har ila yau a cikin shekarar ne sarkin ya karbi bakuncin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Mahmoud Yakubu, wanda ya ba da tabbacin gudanar da nagartacce kuma karbabben zabe a bana.

A dai cikin shekarar ne sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar jajantawa ga ‘yan kasuwar sayar da Wayar hannu ta Beirut Road, bisa iftila’in rushewar wani gini mai hawa uku da ya yi sanadiyyar asarar rayuka.

Idan dai za a iya tunawa a cikin shekarar ne mai martaba sarki ya nada Alhaji Bashir Mahe Bashir a matsayin sabon Walin Kano, da kuma Dakta Mansur Mukhtar Adnan a matsayin sabon sarkin Ban Kano, inda ya ce ya nada su ne bisa cancantarsu, duba da irin gogewarsu a fannoni daban-daban.

A shekarar ta 2022 ne mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana rashin jin dadinsa, saboda rashin shigar wasu kananan hukumomin Jihar Kano gasar musabaka ta kasa.

Haka kuma a shekarar ne Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin manyan baki a fadarsa, da suka hadar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, da ministoci da gwamnoni, sai sarakuna, ciki har da mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.

Sauran sun hada da sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Mamman Dauda, da shugaban jami’ar Bayero da ke nan Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, da shugaban hukumar kidaya ta kasa Alhaji Nasir Isah Kwara, sai mataimakin shugaban bankin raya musulunci na duniya Dakta Muhammad Sulaiman, sai kuma sabon babban jami’in hukumar hana fasakauri ta kasa shiyyar Kano da Jigawa Alhaji Mu’azu Hassan Raji da dai sauransu.

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!