Labarai
Sarki Muhammadu Sunusi II ya yaba da kokarin hukumar Wasani ta Kano

Mai martaba sarkin kano Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya yaba da irin kokarin da hukumar Wasani ta jihar Kano ta ke yi wajen samar da wassanin da Suke Sanya al’umma nishadi.
Sarkin ya bayyana haka ne ta bakin galadiman Kano Alhaji Mannir Sunusi Bayero yayin da yake karbar tawagar shugabanin hukumar Wassani a fadar sarki.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu yace samar da hukumomi Wassani ka iya kawo cigaba a cikin al’umma ya kuma jaddada ta’aziyyarsa ga hukumar bisa rashin da aka samu na Yan wasan Kano su ashirin da biyu da suka rasu a kwanakin baya.
A nasa jawabin shugaban kungiyar Yan Wasan kwallon kwando ta jihar Kano Alhaji Umar Ibrahim Fagge ya ce, sun kai ziyara fadar sarkin ne domin yin ta’aziyyar Yan Wassan jihar da sukayi hadarin mota a kan hanyarsu ta dawowa gidan daga jihar ogun tare da kuma neman sarkin ya zama uban a harkokin Wasanin kwallon kwando na jihar Kano.
Mai martaba sarkin ya na ci gaba da karbar korafen korafen al’umma a fadarsa.
You must be logged in to post a comment Login