Labarai
Sarki Sanusi ya shawarci gwamantin Kano kan ta tabbatar ana hukunta masu kashe mutane

Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya shawarci gwamnatin jihar Kano kan ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin an zartar da hukunci kisa a kan duk wani mutum da aka tabbatar ya na da hannu wajen kisan mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Khalifa Muhammadu Sunus ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kan kisan wata mata da yayanta a unguwar Dorayi Chiranci da ke yankin karamar hukumar Kumbotso.
A wani labarin kuma Mai martaba sarkin Kanon ya yi kira ga hukumar Zakka da hubusi ta jihar da ta dage wajen karbo Zakka a hannu mawadata da manoma don taimaka wa marasa karfi.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da shugaban hukumar zakka da hubusi ta jihar Kano karkashin jagorancin shugabanta Barista Habibu Dan Almajiri Fagge Suka ziyarce shi a fadarsa.
Barista Habibu Dan Almajiri Fagge yace sun zo fada ne don gabatar da kansu da kuma neman alfarmar Mai martaba sarkin daya yi kira ga mawadata kan su rinka taimakawa marasa karfi duba da yanda watan azumi yake gabatowa.
You must be logged in to post a comment Login