Connect with us

Manyan Labarai

Muna goyon bayan ilimi kyauta kuma wajibi -sabon Sarkin Kano

Published

on

Sabon sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jaddada goyon bayan sa ga shirin ilimi kyauta kuma wajibi na gwamnatin jihar Kano.

Mai martaba Aminu Ado Bayero, yace zasu yi duk mai yiwuwa karkashin ikon su don ganin shirin ya tabbata da amfanar da al’umma, san nan ya yi  kira ga dukkanin Al’umma dasu mayar da hankali wajen taimakawa makarantu a wani mataki na bunkasa harkokin ilimi a fadin jihar nan.

Sabon sarkin, ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai makarantan firamare ta gidan makama don duba halin da karatun makarantar yake gudana.

Sabon Sarkin Kano yaje gidan mahaifiyar sa don neman tabarraki

Ana tsaka da nada sabon sarkin Bichi

Mai martaba Aminu Ado Bayero,  ya ce wajibi masu hannu da shuni da  su shigo cikin  harkokin sha’anin ilimi domin kuwa gwamnati kadai baza ta iya ba.

A nasa jawabin shugaban hukumar kula da makarantun sakandire na jihar kano, Dr Bello Shehu,  ya nemi hadin kan  masarautun gargajiya don ganin  shirin ya cimma nasara.

Shamsu Dau Abdullahi, wakilin mu da ya halarci wajen taron  ya ruwaito cewar yayin ziyarar sabon sarkin  ya samu rakiyar manyan hakiman sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,797 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!