Labarai
sarkin gombe ya bukaci shugaban Kwalejin horas da malamai ta jihar ya kula da walwalar ma’aikatan Kwalejin
Mai martaba Sarkin Gombe Dr. Abubakar Shehu Abubakar na Uku, ya yi kira ga sabon shugaban Kwalejin horas da malamai ta jihar Gombe Dakta Ali Adamu Boderi da ya kasance mai gaskiya da rikon amana kula da cigaban ma’aikatan Kwalejin tare da ciyar da ita gaba.
Sarkin na Gombe ya bayyana hakan ne a jiya yayin ziyarar shugabannin gudanarwar Kwalejin karkashin jagorancin sabon shugaban makarantar a fadar sa.
Mai martaba Sarki Abubakar Shehu Abubakar III ya kuma ja kunnen sabon shugaban Kwalejin horas da malaman ta tarayyar kan ya kasance mi kishi da kuma yunkurin wajen ciyar da kwalejin gaba da kuma bayar da gudunmowa wajen samar da ingantaccen ilimi ga al’ummar jihar tare da rike mukamin da Allah ya bashi ba tare da wasa ba don ciyar da kwalejin gaga.
A nasa jawabin kwamishinan matasa na jihar ta Gombe, Alhaji Faruk Jarma cewa ya yi nadin na Dr. Ali Adamu Boderi ya dace la’akari da jajircewar sa wajen aiki.
Shi kuwa Magatakardar Kwalejin Alhaji Umar Bello ya shida wa sarkin na Gombe cewa, sun kai ziyarar ne don bayyana masa godiyar su bisa irin gudunmawar da yake baiwa Kwalejin, tare da neman albarkar fadar ta jihar Gombe.
Da yake nasa jawabin, sabon shugaban Kwalejin Dr Ali Adamu Boderi wanda aka nada shi a makon da ya gabata, ya bayyana cewa, ya karbi kiran na mai martaba hannu biyu-biyu tare da neman hadin kan ma’aikatan da ke karkashin sa don gudanar da aiki yadda ya kamata.
Haka zalika Dr. Ali Adamu Boderi ya kuma sha alwashin ciyar da Kwalejin gaba ba tare da bata lokaci ba.