Connect with us

Labarai

Yawan wadanda suka kamu da Corona ya kai 595 – NCDC

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cuttutuka ta kasa NCDC ta ce an samu karin masu dauke da cutar corona a fadin kasar nan guda 595, yayin da mutane tara  suka rasa rayukansu.

Cibiya ta bayyana hakan ne a shafinta na Twita a daren jiya Alhamis, a yayin da tace adadin wadanda da suka rasa rayukansu a sakamkon cutar a fadin kasar nan suka kai 769.

Ta cikin sanarwar da cibiyar ta fitar ta ce ya zuwa yanzu, masu dauke da cutar a kasar nan sun kai 34,854 yayin da ake jiran sakamokon gwajin mutane 202,97.

Daga cikin jihohin da aka samu karin masu dauke da cutar akwai jihar Lagos mai Mutane 154 sai jihar ondo-95 Rivers-53 Abia-43 Oyo-38 Enugu-29 Edo -24 birnin tarayya Abuja-23.

Sauran sune jihar Kaduna-20 Jihohin Akwa Ibom da Anambra-17 Osun-14 jihar Kano na da 13 jihar Imo-11 Delta -6 Ekiti-5.Gombe (4), Plateau (4), Cross River (2), Adamawa (1), Bauchi (1), Jigawa (1), Yobe (1)

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!