Labarai
Sarkin Hausawan Afrika ya nemi dalibai su koyo sarrafa harshen Hausa
Sarkin Hausawan Afrika kuma Sardaunan Jihar Agadaz Dakta Abdulkadir Labaran Koguna, ya bukaci dalibai da su mayar da hankali wajen koyo tare da sarrafa harshen hausa.
Dakta Abdulkadir Labaran na bayyana hakan a yau ta cikin shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar freedom Rediyo, wanda ya mayar da hankali kan ranar Hausa ta duniya da za a gudanar a gobe Laraba.
Dakta Labaran ya kuma ce, harshen hausa na taka rawa wajen dabbaka al’adun bahaushe, yana mai cewa, matasan yanzu na kokarin aron al’adun wasu harsunan wanda bai daidai ba ne.
A cewar sa, harshen hausa ya mamaye kasashe hamsin da tara a fadin duniya, wanda ya ba su damar yin sarautu a wasu kasashen a bangaren harshen na hausa.
Shi ma da ya kasance cikin shirin, sarkin kungiyar daliban Hausa ta kasa Malam Nura Sulaiman Janburji, ya ce harshen hausa na da alfarma ta yadda a kasashen ketare akan bai wa dalibai damar kafa daula.
Bakin biyu, sun yi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai da su dabbaka harshen hausa a majalisun kasar nan don kare marbatar sa a idon duniya.
You must be logged in to post a comment Login