Labarai
Sarkin Kano da Lamidon Adamawa sun gana da shugabannin Fulani don magance rikicin Fulani makiyaya
Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II da Lamidon Adamawa Muhammadu Mustapha Barkindo da sauran masu ruwa da tsaki sun gana da shugabannin kungiyoyin Fulani a kasar nan domin lalubo hanyar da za a magance rikicin Fulani makiyaya da manoma.
Kungiyoyin da aka gana da su sun hadar da ta Miyatti Allah da kuma Kautal Hore da Gan Allah inda kuma sauran masu ruwa da tsakin da aka tattauna da su suka hadar da Farfesa Ango Abdullahi da kuma Dr Aliyu Tilde.
Da yake jawabi yayin taron da ya gudana Asabar din da ta gabata a Abuja Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ya ce a yanzu haka ana ta kokarin kawo karshen matasalar tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma gwamnati inda kuma ya kira yi kungiyoyin da sa zauna lafiya.
Ya kuma ce taron masu ruwa da tsakin da mambobin gwamnatin tarayya da suka hadar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministan ayyukan gona Chief Audu Ogbe da kuma ministan harkokin cikin gida Abdurrahman Bello Dambazau.
Mai martaba sarkin ya ce yayin taron na jiya ministan ayyukan gona ya amince da aikewa da jami’an ma’aikatar domin su binciki burtalai da makiyaya da ake dasu a kasar nan.
Ya kuma jaddada bukatar da ke akwai ga gwamnatin tarayya na ta tallafawa Fulani makiyaya da abincin dabbobi da kuma ruwa kamar yadda yake wakana a kasashen da suka cin gaba.