Labarai
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jagoranci shugabannin kungiyar fulani ta Duniya zuwa ta’aziyar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mai martaba sarki Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya jagoranci shugabannin kungiyar fulani ta duniya zuwa ta’aziyar tsohon shugaban kasar najeriya marigayi Janar Muhammadu Buhari.
Sarki ya sauki Shugabannin kungiyar fulanin a gidan sa dake jihar kaduna inda daga nan kuma ya jagorance su zuwa gidan marigayin dake Kaduna domin yi musu ta’aziyar marigayin.
Yayin ziyarar ta’aziyar matar marigayi tsohon shugaban kasar Aisha Buhari da babban dansa Yusuf Buhari ne suka karbi ta’aziyar shugabannin fulani inda sarki ya yiwa marigayin addu’a da kuma nema masa gafarar Allah.
Da yake jawabi jagoran kungiyar fulani sarkin Jajere na Jihar Yobe ya bayyana irin girman alakar kungiyar tasu da marigayi janar muhammadu buhari.
Inda yace janar muhammmadu buhari nasu ne kuma wannan kungiya ta Fulani na duniya bazasu manta da irin gudun mawar
You must be logged in to post a comment Login