Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Sarkin Kano na 14 a Daular Fulani Muhammadu Sanusi II ya zama Khalifan Tijjaniyya a Najeriya

Published

on

Darikar Tijjaniyya ta nada Sarkin Kano na 14 a Daular Fulani Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin Khalifan Tijjaniyya a Najeriya.

An gudanar da nadin ne a daren Juma’ar nan a Sokoto, kuma bikin nadin ya samu halartar manyan jiga-jigan darikar ta Tijjaniya a ciki da wajen Najeriya, da suka hada da Sheikh Dahiru Usman Bauchi da kuma gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Muhammadu Sanusi na biyu ya gaji kakansa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daya, wanda shi ne Khalifan Tijjaniyya na farko a Najeriya.

Tun bayan rasuwar Khalifan Tijjaniya Sheikh Isyaka Rabi’u a shekarar 2018 ba nada sabon Khalifa ba sai yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!