Labaran Kano
Sarkin Kano ya ankarar da jama’a kan cutar Lassa
Mai martaba sarkin Kano Mallama Muhammadu Sunusi na II ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar Kano da su kwantar da hankulan su tuni hukumomin lafiya suka dauki matakan da za’a dakile cutar tun bayan bullar zazzabin Lassa a nan jihar Kano.
Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ya bukaci al’ummar jihar Kano da su guji yin amfani da magugunan gargajiya wajen magance cutar Lassa idan wani ya kamu da cutar, mai makon haka su gaggauta zuwa asibiti don duba lafiyar su
Malam Muhammadu Sunusi ya bayyana hakan ne a jawabin sa na mussaman da yayi a fadar sa bayan da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano sanar da cewa an sami bullar cutar zazzabin lassa a jihar Kano.
Kazalika Sarkin ya sake nanata bukatar dake akwai ga duk kan wanda ya sami wani sauyi a jikin say a garziyya zuwa asibiti don duba lafiyar sa don dakile bazuwar cutar ta Lassa a jihar Kano baki daya.
A yayin da yake Ambato wasu daga cikin almomin cutar da likitoci suka bayyana da ya hadar da zazzabi mai zafi da ciwon kai da ciwon kirji da gabobi da gudawa da kuma zubar jini daga hanci, Muhammadu Sunusi na II ya bukaci jama’a su kula da tsaftace mahallan su da kuma kula da kiwon lafiyar su a koda yaushe.