Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Sarkin Kano ya ankarar da jama’a kan cutar Lassa

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Mallama Muhammadu Sunusi na II ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar Kano da su kwantar da hankulan su tuni  hukumomin lafiya suka dauki matakan da za’a dakile cutar tun bayan bullar  zazzabin Lassa a nan jihar Kano.

Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ya  bukaci  al’ummar jihar Kano da su guji yin amfani da magugunan gargajiya wajen magance cutar Lassa idan wani ya kamu da cutar, mai makon haka su gaggauta zuwa asibiti don duba lafiyar su

Malam Muhammadu Sunusi ya bayyana hakan ne a jawabin sa na mussaman da yayi  a fadar sa bayan da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano  sanar da cewa an sami bullar cutar zazzabin lassa a jihar Kano.

Kazalika Sarkin ya sake nanata bukatar dake akwai ga duk kan  wanda ya sami wani sauyi a jikin say a garziyya zuwa asibiti don duba lafiyar sa don dakile bazuwar cutar ta Lassa a jihar Kano baki daya.

A yayin da yake Ambato wasu daga cikin almomin cutar da likitoci suka bayyana da ya hadar da zazzabi mai zafi da ciwon kai da ciwon kirji  da gabobi da gudawa da kuma zubar jini daga hanci, Muhammadu Sunusi na II ya bukaci jama’a su kula da  tsaftace mahallan su da kuma kula da kiwon lafiyar su a koda yaushe.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!