Labarai
Sarkin Kano ya buƙaci gwamnati da masu hali su taimaki talakawa
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga gwamnatoci da mawadata da su tallafa wa marasa ƙarfi domin sauƙaƙa musu matsin rayuwa da a ke fama da shi.
Sarkin ya buƙaci hakan ne wata ganawa da ya yi da manema labarai a fadarsa a wani ɓangare na bikin ranar agaji ta duniya.
Ya ce, “A matsayinmu na shugabani kuma waɗanda ke tare da talakawa kuma muke sauraron koke-kokensu a kullum, ya zama wajibi mu ƙara jan hankalin wadanda ke da wadata su riƙa tallafa wa makobtansu waɗanda ba su da hali”.
A gefe guda kuwa sarkin ya yi bayanin cewa koda a kwanankin baya ya bayyanawa shugaban kasa halin da al’umma ke ciki na matsin rayuwa a wani zama da shugaban ya yi da sarakuna.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login