Labarai
Sarkin Kano ya gana da masu zuba jari daga kasar Sin
A matsayin sa na jagora wajen kawo sauyi a tattalin arziki da kokari kan bunkasa masa’an tun a jihar Kano Sarkin Kano Muhamma Sunusi na II zai karbi bakwancin masu zuba jari daga kasar China da safiyar yau a fadar sa dake kofar Kudu, a nan Kano.
Sai dai ajiya Alhmais ne Muhammadu Sunusi na II CON a matsayin sa na shugaban kwamitin bada shawarwari kan zuba jari ya gana da masu wakiltar manyan kamfanonin biyar dake sha’awar zuba jari daga kasar China a fadar sa.
Ganawar ta sami wakilai daga bankin raya masana’antu da bankin bunkasa kasashen Afrika da masu zuba jari daga nan Kano.
Ganduje da Sarkin Kano sun gana da masu zuba jari daga kasar China
Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa
Tarihin zikirin shekara da ake yi a fadar sarkin Kano
Zulum- ya baiwa malamai 30 kwangilar addu’o’i a kasa mai tsarki
Bayan kamala ganawar ne, masu ruwa da tsaki daban-daban suka sanya hannun yarjiniya da Bankin raya masana’atu da na bunkasa kasashen Afrika.
Haka zalika, wasu daga cikin wakilai daga kasar China wanda gwamnan yankin Shangdon ke jagoranta da kuma wasu wakilai na jam’iyyar Kwamunasanci sun iso nan Kano a wata ziyara ta kwanaki biyu wanda shima za su gana da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II da sauran kososhin gwamnati, da ‘yan kasuwa don samar da damamaki kan kasuwanci a nan Kano
Wakilan dai za su bar jihar Kano a ranar Asabar 9 ga wannan watan na Nuwanba.