Labarai
Sarkin Kano ya naɗa sabon Dagacin Alajawa

Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi ll, ya nada Malam Abubakar Abubakar, a matsayin sabon Dagacin garin Alajawa da ke karamar hukumar Bagwai
Sarkin ya hori sabon Dagacin da ya zauna da jama’arsa lafiya, ya kuma mayar da hankali wajen haɗa kan al’ummarsa tare kuma da bada gudunmuwarsa wajen bada ilimi addini da kuma kula da harkar lafiya a yankunan da ke ƙarƙashinsa.
A nasa jawabin wazirin Kano Alhaji Sa’adu Shehu Gidado Wanda yaja hankali Sabon dagacin garin alajawa daya Sanya idanu kan bakin da Suke shigowa gari ba bisa ka’ida ba.
Sabon Dagacin na garin Alajawa Malam Abubakar Abubakar ya gode wa mai martaba Sarkin Kano bisa bashi wannan sarauta da yayi tare da alkawarin yin iya kokarinsa na ciyar da masarautar Kano gaba.
Haka kuma, mai martaba sarkin ya karbi rahoton ambaliyar ruwa a garin Kunya da Kauke da ke karamar hukumar Minjibir inda aka samu rushewar gidaje da kusam kimanin dari biyu da kuma zaizayar kasa a yankin al’ummar wannan yankin suna neman taimakon sarki da gwamnatin jihar nan dasu kawo musu dauki.
A nasa jawabin, Dagacin garin Kauke Malam Haruna Abubakar ya bayyanawa sarki yanda abun ya faru a yankunan nasu.
You must be logged in to post a comment Login