Connect with us

Labarai

Sarkin Kano ya nemi hadin kan majalisar dokokin jiha don ayyukan ci gaban al’umma

Published

on

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga ‘yan majalisar dokokin jihar kano da su rika taimakawa masarautu domin samun ci gaban al’umma da masarautun jihar biyar.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana haka yayin da tawagar kwamitin kula da masarautu na majalisar dokokin Kano suka kai masa ziyara a fadarsa.

Sarkin ya ce, ziyarar ta su, za ta zamo wani tsani na hada kai da masarautu don kyautata tsaro a dukkanin masarautun biyar.

A nasa jawabin shugaban kwamitin masarautun kuma dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar karaye Nasiru Abdullahi Dutsen Amare ya ce, za su hada kai da dukkanin masarautun don ganin an kawo ci gaban da ya dace.

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma yin alkawarin bada hadin kai wajen samar da tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!