Connect with us

Coronavirus

Sarkin Kano ya nuna tausayinsa game da halin da al’umma suke ciki

Published

on

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna tausayinsa kan halin da al’umma ke ciki sakamakon killace su a gidaje a yakin da ake na dakile annobar Corona a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a wani taro na ‘yan jarida da ya gudana a fadar sarkin na Kano.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su himmatu wajen ganin sun tallafawa kudirin gwamnati na tallafawa marasa karfi a zaman da suke a gida ba tare da fita wajen gudanar da sana’oin su ba.

Abubuwa bakwai da sarkin Kano ya fada kan Lockdown

Sarkin ya ci gaba da cewa a halin yanzu ana samun karuwar masu dauke da annobar Covid-19 a jihar Kano da suka kai kimanin sama da Ashirin.

Yayin taron ‘yan jaridar sarkin na tare da wasu daga cikin hakiman sa da suka hadar da Dankadan Kano da Yan dakan Kano sai kuma hakimin kumbotso da sauran hakimai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,655 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!