Connect with us

Labarai

Mutum na farko da ya kamu da Corona ya isa jihar Jigawa

Published

on

Gwamatin jihar jigawa ta karbi dan asalin jihar mai dauke da cutar COVID-19 daga jihar Kano, duk da cewa ya na daya daga cikin mutane 21 da a ka tabbatar su na da cutar a jihar Kano.

Shugaban kwamatin yaki da yaduwar cutar kuma kwamishinan lafiya na jihar Jigawa Dr. Abba Umar ne ya bayyana hakan ga manema labari a yau juma’a.

Dr. Abba ya kuma kara da cewa sakamakon gwajin mutane 3 da su ka aika hukumar NCDC gwajin ya nuna cewa basa dauke da kwayar cutar.

Wakilin mu a Jigawa Aminu Umar Shuwajo ya rawaito mana cewa, gwamnatin Jigawa ta yi martani kan kalaman shugaban hukumar KAROTA na Kano da ya ce jihar Jigawa bata da kayan aikin kula da masu cutar Coronavirus.

A martanin kwaminshinan ya ce” Duk jihohin Arewa baya jin akwai wata jiha da ta kai jihar Jigawa kayan aikin ko ta kwana kan wannan cuta, domin haka ina kira ga jami’an gwamnati da sauran al’umma su guji yin zance mara tushe bare makama”. Inji Dr Abba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!