Kiwon Lafiya
Sarkin Kano ya sha alwashin inganta fannin Lafiya
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sha alwashin ganin an inganta fannin kiwon lafiyar al’umma a fadin jihar.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karɓi baƙuncin gamayyar shugabanin cibiyar Africa Centre Of Excellence for Population Health and Policy ƙarkashin jagorancin Farfesa Hajiya Hadiza shehu galadanci a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero wanda Madakin kano Alhaji Yusuf Nabahani, ya wakilta, ya bayyana gamsuwarsa bisa ga yadda cibiyar ke samar da ingantacciyar lafiya ga al’ummar jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.
A nata jawabin shugabar cibiyar Farfesa Hajiya Hadiza Shehu Galadanci, ta bayyana cewa an kafa cibiyar ne domin fadakarwa da wayar da kan al’umma don sanin mahimmacin lafiyarsu.
Farfesa Hadiza Galadanci ta kuma ce, cikin ƙananan hukumomin Kano 44 za su fara da guda hudu da suka ƙunshi ƙaramar hukumar Nasarawa da kumbotso da Ungoggo da Gwale.
Yayin ziyarar cibiyar ta samu wakilcin shugabanin fannin lafiya daga jami’ar Bayero da jami’ar Yusuf Maitama Sule da sauransu.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login