Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Musulmi ya bada umarnin duba jinjirin watan Ramadan

Published

on

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, kuma shugaban majalisar kolin harkokin addinin musulunci ta Najeriya, ya umarci al’ummar musulmi da su fara duban jinjirin watan Ramadan daga gobe laraba, 22 ga watan Maris din nan da muke ciki.

Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan mulki na majalisar kolin Alhaji Zubairu Haruna Usman ya fitar.

Sanarwar ta bukaci malamai da su yi amfani da lokutan gudanar da Tafsirai da suke yi a lokacin Azumi wajen wayar da kan al’umma, musamman ma mawadata a kan sakon da Alkur’ani yake dauke da shi wajen tallafa wa marasa karfi.

Haka kuma ya bukaci malamai da su kara kaimi wajen yada duk wani abu da zai kawo zaman lafiya, tare da kawar da duk wani abu da zai janyo rabuwar kai a tsakanin mutane, da kuma yin nasiha a kan yin kyakykyawan shugabanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!