Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dauda Lawal na PDP ya lashe zaben jihar Zamfara

Published

on

Hukumar zabe ta Nijeriya INEC ta ayyana Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Zamfara, bayan da ya kayar da gwamna mai ci Muhammad Bello Matawalle na jam’iyyar APC.

Babban jami’in hukumar ta INEC a jihar Zamfara Kasim Shehu, ne ya sanar da sakamakon da tsakar daren Litinin din makon nan bayan kammala tattara alkaluman zaben.

Dauda Lawal na PDP, ya samu kuri’u dubu dari uku da saba’in da bakwai, da dari bakwai da ashirin da shida.

Shi kuwa gwamna Bello Matawalle na APC, ya samu kuri’u dubu dari uku da goma sha daya, da dari tara da saba’in da shida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!