Kiwon Lafiya
Sashin DPR na daukar matakan dakatar da karkatar da man fetur
Sashin kula da albarkatun man fetur na kasa DPR ya ce ya dauki dukkanin matakan da suka da ce wajen magance matsalar karkatar da manfetur da wasu dillalan man fetur ke yi zuwa kasashen Nijar da Chadi da kuma Benin.
Kwanturolan shiyyar Kaduna Isa Tafida ne ya sanar da hakan ya yin taron manema labarai da ya gudar jiya litinin a jihar ta Kaduna
Isa Tafida ya ce sashin raba albarkatun mai na kasa yana da wadataccen man fetur, da zai iya magance duk wata matsalar mai da za ta iya kunno kai a kasar nan.
A don haka ne ya bukaci al’umma masu sayan mai suna boyewa a halin yanzu sakamakon barazanar da ake yi na cewar za a samu karancin mai, a cewar sa ko kadan babu batun matsalar mai a kasar nan.
Ya kuma ce jami’an sashin na DPR ba za su ragawa ko wanne dillalin mai da ta kama ya na karkatar da mai zuwa wata kasar ba, ko kuma gidan man da ya boye mai da gangan domin wahalar da al’umma.
Ya ce a yanzu haka babu wata tashar dakon mai a kasar nan da bata da wadataccen man fetur a don haka dukkanin gidajen man da suka rufe da sunan ba bu mai, to sun yi ne domin su wahalar da al’umma don kashin kansu.