Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Satar Ɗalibai: Hukumar tsaro ta Civil Defence ta tura jami’ai mata gadin makarantu

Published

on

Hukumar tsaro ta civil defence ta tura da jami’anta mata don gadin makarantu a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

 

Shugaban hukumar, Ahmed Audi, shine ya ba da wannan umarni yayin zantawa da manema labarai a jiya laraba.

 

Ya ce an ɗau wannan mataki ne don kare lafiyar ɗalibai da malamai a makarantu da ke Najeriya.

 

‘‘Yanzu haka jami’an mu mata za su fara gudanar da wani atisaye tare da ɗaukar horo na wata ɗaya kafin su fara aikin nasu na ba da tsaro a makarantun ƙasar nan’’ inji Ahmed Audi.

 

‘‘Wannan mataki dai ya dace da umarnin da  ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya bayar a kwanakin baya.’’ A cewar sa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!