Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Sati biyu kenan babu wanda ya rasu sanadiyyar Corona a Kano – Ganduje

Published

on

Gwammatin jihar Kano ta ce ya zuwa yanzu sati biyu kenan ba a samu ko mutum guda da cutar Corona ta hallaka ba a Kano.

Mataimakin babban jami’in kwamitin karta-kwana kan yakar cutar Corona a Kano Dr. Sabitu Shanono ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake jawabin bayyana halin da ake ciki game da yaki da cutar Corona a Kano.

Ya kara da cewa, kalubalen da suka samu bai wuce na boye bayanai da mutane keyi ba, dangane da cutar, domin gudun kyamata daga al’umma.

Dr. Shanono ya bukaci al’ummar Kano da su daina kyamatar cutar Corona, domin hakan zai dakile kokarin da ake wajen yaki da ita.

A nasa bangaren Dr. Abdullahi Umar Ganduje a yayin taron, ya ce sati daya da ya wuce cikin samfur 3,474 da aka dauka, mutane 56 kacal ne aka samu na dauke da cutar ta Corona.

Ya kara da cewar, akwai bukatar jama’a su cigaba da biyayya ga matakan da masana kiwon lafiya suka sanya domin ganin an dakile yaduwar cutar.

Wakiliyar Freedom Radio a fadar gwamnatin Kano, Zahra’u Nasir ta rawaito cewa a ranar Talatar gwamna Abdullahi Ganduje ya ziyarci cibiyar killace wadanda suka kamu da cutuka masu yaduwa dake ‘Yar Gaya, wadda kamfanin MudaTex ke aikin gyaranta.

*ZN*

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!