Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Saura ƙiris a fara shan jar miya – Buhari

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya ce ƴan Najeriya za su samu sassauci kan halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki da zarar cutar Covid-19 ta wuce.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.

Garba Shehu ya ce, sanadiyyar cutar Corona babu ƙasar da tattalin arziƙinta bai durƙushe ba sai ƙasar China, a don haka halin matsin ba iya Najeriya ya shafa ba.

Duk da haka gwamnatin tarayya na iya ƙoƙarin ta wajen ɗaukar matakan kawo sassauci ga al’umma, kuma muna fatan ba zai ɗore ba sauƙi na nan zuwa cikin yardar Allah a cewarsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!