Connect with us

Labarai

Saura ƙiris na kori Aminu Wali daga PDP – Kwankwaso

Published

on

Jam’iyyar PDP tsagin tsohon gwamna Kwankwaso ta ce, tana kan hanyar korar tsagin Aminu Wali daga jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.

A cewarsa, su ƴan jam’iyyar PDP mai tsintsiya ce, kuma suna kan hanyar korar su.

Sagagin yana martani ne kan matakin tsagin Aminu Walin na korar tsohon gwamna Kwankwaso daga jam’iyyar.

A martanin da ya mayar shugaban jam’iyyar tsagin Aminu Wali Muhamminna Baƙo Lamiɗo ya ce, su ne halastattun shugabannin jam’iyya na jiha, waɗanda suka bi kundin tsarin mulki.

Sai dai tuni uwar jam’iyyar ta ƙasa ta marawa tsagin Kwankwaso baya a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ta Kola Ologbondiyan ya fitar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,693 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!