Labarai
Sauya sheƙa: Kotu ta sauke gwamnan jihar Ebonyi da mataimakinsa
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi da mataimakinsa Eric Kelechi Igwe da su gaggauta ficewa daga ofishinsu bayan sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani hukunci da ya yanke a ranar Talata, ya bayyana cewa bayan ficewa daga jam’iyyar da suka lashe zaɓen.
Mai shari’a Ekwo ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta karɓi sunayen mambobinta daga hannun jam’iyyar PDP domin maye gurbin Umahi da Igwe, domin cike ragowar wa’adin mulkinsu, ko kuma ta sake gudanar da sabon zaɓe domin maye gurbin nasu.
Alƙalin kotun ya kuma haramtawa Umahi da Igwe ci gaba da bayyana kan su a matsayin gwamna da ataimakin gwamnan Jihar Ebonyi.
You must be logged in to post a comment Login