Labarai
Sauya sheka: Kotu ta kori ƴan masajalisa 20 a Cross River
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da wasu ƴan majalisar dokokin jihar Cross River su 20 da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa jam’iyyar APC.
Ƴan majalisar dai sun fice daga jam’iyyar PDP ne tare da Gwamna Ben Ayade, wanda ya ce ya koma jam’iyya mai mulki ne domin marawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari baya domin gina ƙasa.
Da yake yanke hukunci a ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar, Mai shari’a Taiwo Taiwo ya umurci ƴan majalisun da su bar ofishin su saboda sun yi watsi da jam’iyyar da suka samu nasarar hawa kan karagar mulkin.
Lamarin dai na zuwa ne makonni kaɗan bayan da kotu ta kori Gwamna David Umahi na Ebonyi da mataimakinsa da wasu ƴan majalisar dokokin jihar saboda sun sauya sheƙa.
You must be logged in to post a comment Login