Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Schalke 04 ta sallami mai horar da tawagar Wagner

Published

on

Ƙungiyar Schalke 04, da ke ƙasar Jamus ta sallami mai horar da tawagar David Wagner, bayan wasanni biyu da fara gasar Bundesliga ta ƙasar.

Hakan ya biyo bayan rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a wasannin biyu wanda Bayern Munich ta lallasa ta da ci 8 da nema , yayin da Werder Bremen ta doke ta da ci 3 da 1, a wasan da ya gudana a ranar Asabar.

Tsohon mai horar da kungiyar Huddersfield Town, Wagner ya karɓi aiki ne a dab da fara gasar shekarar bana ta 2020/21, sai dai ya fara da rashin nasara guda biyu.

Ƙungiyar ta Schalke 04, ta kasa samun nasara a wasanni 18 na gasar Bundesliga, wanda hakan ya sa ta kafa sabon tarihi a ƙungiyar da mai horar war.

“Muna da yakinin za mu samu ci gaba tare da mai horar wa David Wagner, sai dai kuma an samu akasin hakan kasancewar ga yadda wasannin mu ke tafiya da rashin nasara” .

Don haka mun yanke shawarar buɗe sabon Babi na sallamar, mai horar wa Wagner da mataimakan sa Christoph Buhler da Frank Frohling, muna yi musu fatan alheri a gaba “inji shugaban sashen wasanni na Schalke 04 , Jochein Schneider.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!