Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

SEDSAC ta goyi bayan dokar hukumar FRSC

Published

on

Kungiyar da ke rajin bunkasa harkokin ilimi da kawo daidaito tsakanin al’umma, SEDSAC ta yaba da matakin da hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa FRSC, ta dauka, na fara hukunta jama’a, wadanda ba jami’an gwamnati ba, kuma su ke amfani da Jiniya ko kuma yin kwanbar motoci akan tituna.

Shugaban kungiyar Kwamared Umar Hafizu kofar Nai’sa ne ya bayyana haka, yayin zantawarsa da Freedom Radio da yammacin ranar Alhamis 9 ga watan Janairun 2020.

Ya ce, dama wannan al’amari ya dade yana ciwa mutane tuwo a kwarya, saboda haka yin wannan doka, zai taimaka sosai wajen rage abkuwar hadurra da kuma kyautata tsaro a Najeriya.

Kwamared Umar Hafiz Kofar Naisa ya kuma shawarci masu aikata wannan dabi’ar ta yin kwambar motoci akan tituna ko kuma amfani da motoci masu jiniya, da su guji yin hakan, domin kuwa ya saba wa doka kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Shugaban kungiyar ta SEDSAC, ya kuma yi fatan wannan mataki da aka kudiri dauka zai taimaka matuka wajen tsaftace yadda jama’a ke amfani da tituna a Najeriya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!