Labarai
SERAP ta bukaci shugaban NNPCL ya binciko wadanda suka karkatar da kudaden Mai

Shirin tabbatar da ganin gwamnati na bin ka’idoji wajen gudanar da ayyukanta SERAP ta bukaci babban jami’in gudanarwa na Kamfanin Mai na Ƙasa Bayo Ojulari da ya gano wadanda ke da hannu wajen karkatar da kudaden man da ake zargi sun bace kimanin Sama da Naira Biiyan 22 tare da mikawa Hukumar EFCC da ICPC domin gurfanar da su a gaban kotu.
SERAP ta kuma nemi a dawo da dukkan kudaden da suka ɓace cikin baitulmalin ƙasa ba tare da wani jinkiri ba, tana mai cewa kamata ya yi gwamnati ta dauki matakin gaggawa wajen kare dukiyar jama’a da hana irin wannan al’amari sake faruwa.
SERAP ta bayyana haka ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 25 ga Oktoba, 2025, wacce mataimakin darakta na kungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu.
Rahoton na zargin bacewar kudaden ya fito ne daga rahoton shekara ta 2022 da Auditor-General na Ƙasa ya wallafa a ranar 9 ga Satumba, 2025.
You must be logged in to post a comment Login