Labarai
Shalkwatar tsaro ta ayyana neman mutane 8 da ta ke zargi da kashe sojoji a Delta
Shalkwatar tsaron Nijeriya ta ayyana neman wasu mutane takwas ruwa a jallo wadanda ta ke zarginsu da hannu a kisan sojoji 17 a yankin Okuama na jihar Delta.
Daraktan yaɗa labaran shalkwatar Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a shalkwatar tsaron da ke birnin tarayya Abuja.
Yayin taron dai, shalkwatar tsaron ta fitar da sunayen mutanen takwas da suka haɗa da Farfesa Ekpekpo Arthur da Andaowei Dennis Bakriri da Akevwru Daniel Omotegbo.
Sauran sun hada da Akata Malawa David da Sinclear Oliki da Clement Ikolo Ogenerukeywe da Reuben Baru da kuma Igoli Ebi.
Manjo Janar Edward Buba, ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da kuma sarakunan gargajiya a faɗin Nijeriya musamman a yankin na Neja Delta da su taimaka wa sojoji wajen zaƙulo waɗanda aka bayyana neman nasu ruwa a jallo.
Idan za a iya tunawa a ranar 14 ga wannan watan da muke ciki na Maris ne wasu ɓata-gari suka afka wa sojojin da ke aikin kwantar da tarzoma tsakanin al’umomin yankunan Okuoma da Okoloba inda suka yi musu mummunan kisan gilla.
You must be logged in to post a comment Login