Labarai
Sharuɗan da Doguwa ya sanyawa Kwankwaso domin yin sulhu
Shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwa ya sanya sharuɗa ga tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso.
Sharuɗan da ya sanya sune, ko dai Kwankwaso ya aiko wakilcin mutane biyu su yi masa ta’aziyyar rashin mahaifinsa.
Ko kuma Kwankwason ya kira shi a waya yayi masa ta’aziyyar.
Alhassan Ado ya ce, rashin ta’aziyyar mahaifinsa, shi ne babban laifin da Kwankwaso ya yi masa.
Ya ce, Kwankwaso ba abin yarwa ba ne a Kano.
Kuma garin Kwankwaso shi ne garin mahaifiyarsa, garin mutanen kirki masu ilimi inji Doguwa.
You must be logged in to post a comment Login