Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sheikh Daurawa ya musanta zargin yin rawa a gidan biki

Published

on

Malam  Aminu Ibrahim Daurawa, ya musanta zargin yayi rawa da mai dakin sa a wajen wani biki bayan da aka hasko shi a cikin wani fefen bidiyo rike da hannun ta.

Fefen bidiyo wanda ya karade shafukan sada zumunata anga malamin rike da hannun wata mace suna dansewa, wacce aka yi hasashen cewar mai dakin sa ce, amma malamin ya musanta wannan zargin.

Sai dai  malamin a shafin sa na Facebook ya wallafa cewa bashi ne a waccen fefen bidiyon ba da ake yadawa, bai kuma san waccen mutumin dake cikin bidoyon ba hasalima bashi da gami ko miskala zaratan da shi wanccen mutumin.

Sheikh Aminu Daurawa wanda ya wallafa sakon a shafin san a sada zumunta yana kasa mai tsarki wato Saudiyya ya rantsi kan cewa bashi ne a cikin bidiyon ba, amma yana ganin cewa kila kamace kawai da shi da mutumin da aka gani.

Fefen bidiyon wanda aka yi ta tafka mahawara akan shi a shafukan sada zumunta, ya jan hankali sosai bayan da aka ga malamin ya rike hannun wata mace da ake ganin cewa matar sa shi yana juyi suna rawa tare.

Masu tafka mahawara na ganin cewar bai dace malamin yayi rawa ko da maidakin sa ce a tsakiyar mat aba, yayin da wasu ke ganin cewar ai ba wani abu bane tun da dai matarsa ce ta halal.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!