Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jam’iyyar APC ta dakatar da shugabanta Dr. Abdullahi Abdullahi Umar Ganduje

Published

on

Jam’iyyar APC mai mulki ta mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, a jihar Kano, ta dakatar da shugabanta na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga kasancewarsa mambanta.

Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar ta Ganduje Haladu Gwanjon, ne ya sanar da dakatar da shugaban na kasa a wani taron manema labarai a Kano, ranar Litinin.

Gwanjo ya ce matakin dakatar da Dr Ganduje daga jam’iyyar ya biyo bayan karbar cin hanci da rashawa lokacin yana gwamnan jihar Kano.

A cewarsa, sun yanke shawarar dakatar da shugaban na kasa ne bayan da aka kada masa kuri’a saboda rashin iya wanke sunansa daga wasu zarge-zarge da ake yi masa na cin hanci da rashawa, wadanda suka hada da bidiyoyin daloli da ake yadawa inda ake zarginsa da aikata laifin. karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila

Ya ce dakatarwar ta fara aiki ne daga yau 15 ga Afrilu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!