Labarai
Shigowar baƙin al’adu ya dakushe tasirin Tashe a ƙasar Hausa – Usman Adamu
Wani malami a tsangayar nazarin Harsuna a kwalejin Sa’adatu Rimi ya ɗora alhakin dakushewar al’adar tashe da shigowar baƙin al’adu.
Malam Usman Adamu ya kuma ce, aro baƙin ɗabi’u musamman na Turawa ya taka rawa wajen koma bayan al’adun Hausawa
A zantawar Malam Usman Adamu da wakiliyar Freedom Radio Ummulkhairi Rabi’u Yusuf ya ce “Al’adar tashe daɗaɗɗiyar al’ada ce da Hausawa suke yinta a lokacin azumi wadda tarihi ya nuna cewa ta samo asali daga addinin gargajiya na maguzanci”.
“Bayan zuwan addinin musulunci ne ya zamanantar da shi daidai da tsarinsa, wanda matasa da yara ne suka fi yinsa, don kwaikwayon rayuwa ta zahiri cikin nuni da nishaɗi” a cewar Malamin.
Malam Usman Adamu ya kuma ce “Zamani yazo yanzu tashen ba shi da tasiri saboda wasu dalilai da suka haɗar da gushewar al’adu da rashin tsaro da kuma tasirin kafafen sadarwar zamani”.
“Amfanin tashe kuwa ga Bahaushe yana sanya nishadi kuma yana nuna rayuwar al’umma kai tsaye da zamantakewa, don haka gushewar wannan al’ada ta tashe ba karamin tasirin zai ba wajen haifar da koma baya a al’adun bahaushe”.
Ana dai fara gudanar da al’adar tashe ne tun a ranar 10 ga watan azumin Ramadan domin bunkasa al’adar Bahaushe.
You must be logged in to post a comment Login