Manyan Labarai
Shin rigimar Ganduje da Kwankwaso tazo karshe?
A ranar 21 ga watan Oktoban da muke ciki ne tsohon Gwamnan jahar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya cika shekaru 63 a Duniya.
Bikin ranar cikar tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya shekara 63 ya kawo abubuwa da dama da suka hada da yin abubuwa da suka shafi bikin haihuwar ta sa.
Lokacin da ake bikin na tsohon Gwamna Inijiya Rabiu Musa Kwankwaso sai ga shi wani abun mamaki ya bayyana inda tsohon abokin sa da suka kusa shekaru ashirin suna siyasa tare, wato Gwamnan Kano mai ci a yanzu, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana a shafin wata shararriyar jarida yana taya tsohon mai gidan nasa a siyasa murnar cikar sa shekaru 63 a Duniya.
Wannan sako na taya tsohon Gwamnan na Kano kuma tsohon abokin siyasar Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje a siyasance murna ranar haihuwa ya bawa al’umma da dama mamaki, sakamakon rashin ga miciji da manyan ‘’yan siyasar biyu na jahar Kano ke yi tun sanda dagantakar ta su tayi tsamari.
Shi dai tsohon Gwamnan jahar Kano inijinya Rabiu Musa Kwankwaso ne a watan Nuwambar shekarar 2014 ranar alhamis 27 ga watan na Nuwamba a taro da ya gudana a dakin taro na Afrika House ,ya nuna tsohon mataimakin sa a matsayin wanda zai yi takara shi kadai daga tsagin tsohuwar darikar Gwanma Abdullahi Umar Ganduje wato darikar ta Kwankwasiyya a jamiyyar APC ,dan tunkarar babban zaben Najeriya da ake sa ran gudanarwa a shekarar 2015.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi takarar neman tsayawa Gwamna a zaben fitar da gwani da jamiyyar APC ta gudanar a ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 2014.
Daga cikin wanda suka nemi takarar Gwamna da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje akwai Sakataran gwamnatin jahar Kano na yanzu ,Alhaji Usman Alhaji da kuma tsohon dan majalisar wakilai kuma wanda ya taba bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara akan harkokin majalisa wato Honorable Abdurrahman Kawu Sumaila .
Dab ,da zaa fara zaben fitar da gwanin wasu daga cikin ‘’yan takarar suka janye, da suka hada da shi sakataran gwamnatin na jahar Kano Alhaji Usman Alhaji tare da Abdurrahman Kawu Sumaila.
Da aka cigaba da kokarin fitar da gwani tsohon kantoman mulkin soja na Jahar Kaduna mai ritaya Birgediya Janar Lawal Jaafaru Isa ne ya tsaya takara da Gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda Gwamna Ganduje yayi nasara a fitar da gwani da jamiyyar ta APC din tayi ,
Bayan shiga zaben shekarar 2015 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi nasara.
An rantsar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015 bayan tsohon Gwamna Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya mika masa mulki.
Kafin sabuwar shekarar 2016 ne ake ta rade radin akwai rigima ta siyasa tsakanin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci Dr Abdullahi Umar Ganduje ,
Kwatsam sai lokacin da mahaifiyar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ta rasu, sakamakon zuwa gaisuwa da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi ,Gwamnatin ta jahar Kano ta zarge shi da rashin da’a ,har jamiyyar APC tace zata ladabtar da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso akan diban wadanda ake zargi ‘’yandaba ne zuwa gaisuwar mahaifiyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Tun daga wannan lokaci ne aka fada rikicin siyasa tsakanin Gwamna Abdulahi Umar Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta cigaba da ruruwa har dab da zaben shekarar bana.
A shekarar 2018 ce dai tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya koma tsohuwar jamiyyar sa ta PDP, inda daga nan ne rikicin siyasar ta jahar Kano bata tsagaita ba ,har bayan zaben na shekarar 2019.
Amma sai ga shi kwatsam a ranar 21 ga wata Gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon Gwamnan na Kano kuma tsohon shugaban sa, a siyasa injiniya Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 63 a Duniya.