Labaran Kano
Kano: zan tsoma baki kan rikicin Sarkin Kano da Ganduje – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zayyanu wasu dalilan da suka sanya ba zai tsuma baki kan rikicin masarautar Kano ba.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da yake tarbayar tawagar wasu ‘yan jihar Kano wanda gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta da suka kai masa a fadar sa dake Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai taimakawa shugaban kasa shawara na mussaman kan kafafan yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar cewa, cikin tawagar ta hada da ‘yan siyasa da kososhin gwamnati da masu rike da masarautun gargajiya da ya hada da Sarkin Bichi Aminu Ado Byaero.
Rahotanin sun bayyana cewar, makasudun ziyarar da gwamnan Abdullahi Umar ya jagoraran ta zuwar fadar shugaban shi ne don nuna nasarar da jam’iyyar APC ta samu a jihar Kano da na ‘yan majalisar dokoki ciki har da nasarar da shugaban masu rinjaye na majalisar ya samu ALhassan Ado Duguwa a dai duk zaben.
A cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya ya rataya a wuyan sa, a don haka zai yi duk mai yuwa wajen ganin ya shiga tsakani a rikicin masarautar Kano, in har hakan na barazana ga rayuwar ‘yan asalin jihar Kano da ma kasa baki daya.
Ka zalika shugaban kasa Muhammdu Buhari ya kara da cewar ‘ Na san karfin ikon da nake da shi a matsayi na shugaban kasa wanda kundin tsarin mulkin kasar nan ya bani, kuma gwamnan jihar Kano na da nashi rawar da zai takawa’’
Muhammadu Buhari ya sake bayyana cewar batun na gaban majalisar dokoki ta jihar Kano a don haka sai sun kamala na su kokarin ne zan iya tsuma baki na.
A dai ranar Alhamis daya gabata ne kamfanin dilancin labaru na kasa ya rawaito cewar Sarkin Ningi Alhaji Yunus Danyaya ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceto halin da masarautun gargajiya suka shiga wajen rushe su a yankin Arewacin kasar nan ta hanyar shiga tsakani a rikicin dake tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II
Sarkin Ningin ya bayyana hakan ne a fadar sa a lokacin da yake ganawa da manema labarai cewa, Ina rokar shugaba buhari a matsayin sa na uba da ya yiwa Allah yayi wa Annabi ya shiga tsakani kan matsalolin da jihar Kano ke ciki a halin yanzu wajen daita-daita tsakanin Sarkin Kano da gwamnan jihar Kano”