Labarai
Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi
Ana shirye shiryen yiwa dabbobi sama da Miliyan daya duk shekara allurar rigakafi a jihar Kano wanda za ‘a fara shirin a watan Nuwamba mai kamawa na shekarar bana.
Shugaban shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano, karkashin Bankin Musulunci Malam Ibrahim Garba ne ya bayyana haka.
A wata takarda da Kakakin shirin na jihar Kano, Ameen Kabir Yassar , ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai , Malam Ibrahim Garba , ya ce shirin anyi shi ne don samar da lafiyar dabbobin tare da kawar da barkewar cututtuka masu yaduwa a tsakanin dabbobin tare da kare lafiyar masu kula dasu.
Don haka wajibi ne , yin hakan tare da lafiyar su ta hanyar kare su da tabbatar da basu yada cututtuka ga masu kula dasu ba ko kiwon su.
Malam Ibrahim Garba, ya bayyana hakan ne a ofishin sa a lokacin da ya karbi shugaban kungiyar masu samar da Madara Usman Abdullahi Usman ,tare da wasu Mambobin kungiyar Watari da Doguwa tare da Falgore.
Malam Ibrahim Garba, ya kara dacewa allurar nada cikin shiri da akayi a aiyyukan da shirin zai gudanar kasancewar zai taimaka wajen dakile matsalolin da ake samu wajen yawaitar samar da Madara da Nama, kana yace shirin zai samar da hanyoyin bunkasa saye da siyarwa na kasuwanci ,ta hanyar samar da kasuwannin Shanu, wajen tara Madara ,da dakin gwaje gwaje na dabbobin a yunkurin bunkasa harkokin noma da kiwo a jiha.
Da yake nasa jawabin shugaban shugaban kungiyar masu samar da Madara ta jiha Usman Abdullahi Usman , ya ce makasudin zuwan nasu shi ne don tattauna yadda masu samar da Madara zasu shiga cikin shirin ,tare da hadin gwiwa tsakani don samar da cigaba.
Ya kuma yi kira da shirin ya duba yiwuwar saka hannun jari wajen bunkasawa da samar wa tare da kasuwancin Madara da ake samarwa ta matsakaita don samun mai inganci da Gina jiki tare da koshin Lafiya.
You must be logged in to post a comment Login