Connect with us

Coronavirus

Covid: Sama da mutum 500,000 ne suka mutu a fadin duniya

Published

on

Sama da mutum miliyan 10 ne suka kamu da cutar Covid-19 a fadin duniya yanzu haka, yayinda kididdigar hukumomin lafiya suka tabbatar da cewa sama da 500,000 ne suka mutu sakamakon annobar.

A cewar wani rahoto da jami’ar Johns Hopkins da ke kasar Amurka ta fitar, ana samun karin kididdigar mutanen da ke mutuwa sakamakon annobar, duk da kokarin gwamnatoci na shawo kan matsalar.

Nahiyar turai ce dai yanzu haka ta zama matattarar annobar, yayinda aka fi samun adadin mutanen da ke kamuwa da cutar daga yankin.

Amurka ce dai har yanzu kan gaba na adadin wadanda ke mutuwa sakamakon Covid-19 a nahiyar turai.

Sakataren harkokin lafiya na Amurka, Alex Azar ya yi gargadin cewa akwai sauran rina a kaba kan yadda za a tsaurara matakan magance annobar ta covid-19.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 328,732 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!